5 Agusta 2019 - 07:05
​Libya: Dakarun Haftar Sun Kashe Fararen Hula 20

Jiragen Yakin Khalifa Haftar Sun kai hari kan wani wurin bikin aure tare da kashe akalla fararen hula 20 a Libiya.

(ABNA24.com) Jiragen Yakin Khalifa Haftar Sun kai hari kan wani wurin bikin aure tare da kashe akalla fararen hula 20 a Libiya.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli na kasar Turkiya ya habarta cewa jiragen yaki maras matuki na dakarun Khalifa Haftar sun yi luguden wuta har sau hudu wajen taron bikin aure a garin Murzuq dake yammacin kasar lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla fararen hula 20 da kuma jikkata wasu 35 na daban.

Kafin hakan dai, a watanin da suka gabata, jiragen yakin na dakarun Halifa Haftar sun kai irin wannan hari a wani sansani da aka tsugunar da 'yan gudun hijra na kasashen Afirka a birnin Tripoli tare da kashe mutum sama da 40 daga cikinsu.

Tun a shekarar 2011 ne kasar Libiya ta fada cikin rikici, bayan da kasar Amurka gami da wasu kasashe Turai suka kifar da gwamnatin marigayi kanal Mu'amar Ghaddafi tare da taimakon wasu 'yan kasar da suka yi wa gwamnatin bore.



/129